Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna

A ranar Litinin ne Rundunar 'yan sandan Najeriya suka tabbatar da sace malamin addinin Kirista, Rabarand Fada John Bako da akayi a kauyen Ankuwa da ke karamar hukumar Kachia na jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa Kakakin Rundunar 'Yan sanda, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN lamarin a daren jiya Litinin a Kaduna.

Sabo ya ce rahotannin da rundunar ta samu daga ofishinta na Kachia ya nuna cewa wasu 'yan bindiga ne su kayi kutse cikin gidan malamin addinin misalin karfe 8 na dare su kayi awon gaba da shi.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya bayyana abinda zai yiwa wadanda ba su zabe shi ba

Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna
Da duminsa: 'Yan sanda sun tabbatar da sace babban malamin addini a Kaduna
Asali: Twitter

Ya ce an baza tawagar 'yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane karkashin jagorancin 'yan sandan Kachia domin bin sahun 'yan bindigan da niyyar ceto malamain addinin.

Kakakin 'yan sandan ya ce Kwamishinan 'yan sanda, Ahmad Abdurrahaman yana dukkan mai yiwuwa domin ganin an kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

Ya kuma yi kira ga al'umma su taimakawa rundunar da bayyanai masu amfani da za su iya taimaka musu wurin gano wadanda suka sace malamin addinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel