Buhari da Jonathan sun yi magana bayan Gabriel Okara ya rasu yana da shekaru 97

Buhari da Jonathan sun yi magana bayan Gabriel Okara ya rasu yana da shekaru 97

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ji takaicin rasuwar Gabriel Okara

- Okara fitaccen Marubuci ne kuma babban Mawaki wanda ya shahara

- Gabriel Okara ya rasu ne a babban asibitin gwamnati da ke Yenagoa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta’aziyyar sa a game da rashin babban Mawakin nan kuma Marubucin Najeriya watau Gabriel Okara wanda ya rasu Ranar Lahadin da ta wuce 24 ga Watan Maris a cikin jihar Bayelsa.

Gabriel Okara ya cika ne shekaran jiya a asibitin tarayya da ke Garin Yenagoa na jihar Bayelsa. Okara ya rasu yana da shekaru 97 a Duniya. Shugaba Buhari ya aikawa Iyalin mamacin ta’aziyyar sa ne ta hannun Hadimin sa Femi Adesina.

KU KARANTA: Wani Lauya a barazanar kai Gwamnatin Shugaba Buhari Kotu

Buhari da Jonathan sun yi magana bayan Gabriel Okara ya rasu yana da shekaru 97
Tauraro Gabriel Okara ya rasu yana da shekaru 97 da haihuwa
Asali: UGC

A wani jawabi da Mista Femi Adesina ya fitar Ranar Litinin, yace shugaba Buhari yana bai wa Iyalin Okara hakuri na wannan babban rashi da su kayi. Shugaban kasar yayi addu’a ga Ubangiji ya ba Magadan hakurin jure wannan rashi.

Mai magana da yawun bakin shugaba Buhari, yake cewa ba za a taba mantawa da irin gagarumar gudumuwar da Marigayi Okara ya kawowa Nahiyar Afrika ba. Marigayin ya fito ne daga Kabilar Ijaw, inda yayi rubuce-rubuce da dama.

Haka kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ya fito daga shiyyar Marigayin ya aika sakon gaisuwar sa ga dangin Gabriel Okara. Yanzu haka dai gwamnatin Bayelsa ta bada makokin kwana 3 domin tunawa da Dattijon.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel