Osun: Dallin da yasa Adeleke ba zai iya samun takardar shadar cin zabe ba a yanzu – INEC

Osun: Dallin da yasa Adeleke ba zai iya samun takardar shadar cin zabe ba a yanzu – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace tana iya bai wa Sanata Ademola Adeleke na jam’yyar Peoples Democratic Party (PDP) takardar shaidar cin zabe, idan har gwamnan jihar mai ci, Gboyega Oyetola yaki daukaka kara akan hukuncin da kotun zabe ta yanke na dakatar da shi a cikin kwanaki 21.

A ranar Juma’an da ya gabata ne kotun sauraron karan zaben gwamnan jihar Osun da ke da zama a Abuja ta yanke hukunci, inda ta soke zaben Oyetola na jam’iyyar Progressives Congress (APC) sannan ta kaddamar da Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na 2018.

Justis Peter Obiora wanda ya yanke hukunci yayi umurni ga INEC kan tay gaggawan bayar da wani sabon takardar shaidar cin zabe ga Adeleke a matsayin sahhin zababben gwamna a jihar Osun, bayan ta kaddamar da zaben da aka sake yi a ranar 27 ga watan Satumba, 2018 a matsayin ba bisa doka ba.

Osun: Dallin da yasa Adeleke ba zai iya samun takardar shadar cin zabe ba a yanzu – INEC
Osun: Dallin da yasa Adeleke ba zai iya samun takardar shadar cin zabe ba a yanzu – INEC
Asali: Depositphotos

A jiya, Litinin ne ake ta rade-radi a kafofin watsa labarai tare da hotunan da ke nuni ga cewa INEC ta bai wa Adeleke takardar shaidar cin zabe.

KU KARANTA KUMA: An cire hotunan Sarki Sanusi II daga babban dakin taron Kano

Amma duba ga sashi 143(1) na dokar zabe na 2010, duk dan takarar da aka soke zaben shi yana da damar da zai daukaka kara cikin kwanaki 21 daga ranar da kotu ta yanke hukunci.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa idan har Oyetola ya gaza daukaka kara, INEC zata zama bata da wani zabi da ya wuce ba Adeleke takardar shaidar cn zabe bayan cikar kwanaki 21.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel