Jihar Bauchi: Gwamnan Mohammed Abubakar ya kira Kauran Bauchi, ya tayashi murna

Jihar Bauchi: Gwamnan Mohammed Abubakar ya kira Kauran Bauchi, ya tayashi murna

Gwamnan jihar Bauchi, Abdullahi Abubakar ya aikawa zababban gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammad, sako domin tayashi murnan nasarar da ya samu a zaben 9 da 23 ga watan Maris, 2019.

Wannan na kunshe cikin jawabin babban hadimin gwamnan kan kafafan yada labarai, Ali M. Ali, ranar Litinin, 26 ga wwatan Maris, 2019.

Yace: "Ina taya dan uwana , Sanata Bala, murnan nasara a zabe. Ina farin cikin cewa duk da irin yakin neman zaben da mukayi a jiharmu, an gudanar da zaben lumana ba tare da zub da jini ba."

"Saboda haka ina kira ga zabebben gwamnan ya hada kai da ni wajen shirye-shiryen mika ragamar mulki cikin kwanciyan hankali."

"Ina matukar godewa dukkan mutan jihar Bauchi kan goyon bayan da suka nunawa gwamnatina, kuma ina kira garesu su baiwa gwamnati mai jiran gado irin goyon bayan."

"Kana ina kira da zababben gwamnan ya jawo hankalin mabiyansa su bi doka yayin murnar nasara tunda lokacin yakin neman zabe ya wuce."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nada Jauro sabon shugaban NESREA

Mun kawo muku rahoton cewa Sanata Bala Mohammed, dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya lashe zaben kujerar gwamna bayan an kai ruwa rana tsakanin sa da gwamna mai ci, Mohammed Abubakar, na jam'iyyar APC.

Bayan tattara sakamako da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta yi a yammacin ranar Litinin, an sanar da Bala Mohammed a matsayin wanda ya samu nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Bauchi.

Dakta Musa Dahiru, sabon baturen INEC, ya ce PDP ta samu kuri'u 39,225 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 30,055 daga sakamakon zaben raba gardama da aka yi a jihar Bauchi.\

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel