An cire hotunan Sarki Sanusi II daga babban dakin taron Kano

An cire hotunan Sarki Sanusi II daga babban dakin taron Kano

Mun samu labari cewa, bayan APC ta lashe zaben gwamnan Kano, an samu wasu da su ka sauke hoton Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga cikin babban dakin nan da ake nada sabon Sarki a jihar.

Kamar yadda wani bidiyo ya zo mana, an ga wadannan mutane su na murna yayin da wani kuma ya hau wata kwaranga yana tsige hoton Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da ke cikin wannan dakin taro.

Wannan abu ya faru ne a karshen makon da ya gabata bayan da hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC ta sanar da cewa gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ya koma kan karagar mulkin sa.

KU KARANTA: Tsohon Sanata ya bayyana abin da ya faru a zaben Kano (Bidiyo)

Watakila wadanda su kayi wannan danyen aiki, Magoya bayan gwamna Ganduje ne. Kwanakin baya har wani babban Hadimin gwamnan Kano ya bayyana cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya nuna cewa yana tare da PDP a Jihar.

Wannan mai ba gwamna shawara yake cewa ya kamata Sarkin ya fito ya sa jan rawani kurum a huta inda yake nufin cewa Mai Martaba yana goyon bayan Mabiya tsohon gwamna Rabiu kwankwaso watau ‘Yan Kwankwasiyya.

A kwanakin baya dai an yi ta yunkurin tsige Sarkin Kano inda jita-jita ya zo cewa har sai da ta kai wasu manya sun sa baki tsakanin rikicin na Sarki da kuma gwamnatin Jihar. Wannan karo Sarkin ya nemi ayi adalci ne a zaben na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel