Mataimakin Shugaban kasa ya jagoranci addu’ar farin cikin nasarar 2019

Mataimakin Shugaban kasa ya jagoranci addu’ar farin cikin nasarar 2019

Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa mataimakin shugaban kasa watay Farfesa Yemi Osinbajo da kuma wasu manya na jam’iyyar APC sun godewa Allah game da nasarar da APC tayi a 2019.

Gwamnan Legas mai shirin barin-gado, Mista Akinwunmi Ambode, da kuma Takwaran sa na jihar Oyo watau Abiola Ajimobi su na tare da Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo a wani dakin addu’a da ke filin Obafemi Awolowo a jihar Ogun.

An yi wannan taron addu’o’i na murna ne a ainihin Garin mataimakin shugaban kasar na Ikenne da ke jihar Ogun. Mai dakin mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo tana cikin wadanda aka yi wannan addu’a ta musamman da ita.

KU KARANTA: 'Dan Majalisan Arewa yayi zama da Buhari a game da kujerar Dogara

Mataimakin Shugaban kasa ya jagoranci addu’ar farin cikin nasarar 2019
Mai Girma Mataimakin Shugaban kasa a wajen wani taro
Asali: Facebook

Sauran manyan jam’iyyar APC da su ka halarci wannan ibada sun hada da gwamnan jihar Ogun mai jiran gado a yanzu watau Dapo Abiodun, da kuma tsohon gwamna kuma Sanatan Akwa-Ibom da ya koma APC, Cif Godswill Akpabio.

Tsohon Sanatan Legas wanda yayi Minista a lokacin mulkin Goodluck Jonathan, Musiliu Obanikoro ya halarci wannan gagarumin zaman addu’o’i da godewa Ubangiji Mai girma da aka yi a cikin Jihar Ogun saboda murnar Buhari zai zarce.

Kun ji cewa a karshe an samu Obasanjo yayi magana game da zaben 2019, inda yayi kaca-kaca da masu hana Atiku zuwa Kotu. Tsohon Shugaba Obasanjo ya nuna Atiku zai iya samun nasara idan ya tafi kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel