Tsagerancin 'Yan siyasa ya sa Sojoji suka mu'amalanci zaben 2019 - Felix Omobude

Tsagerancin 'Yan siyasa ya sa Sojoji suka mu'amalanci zaben 2019 - Felix Omobude

Ba ya daga cikin tsari da tanadin kowace kasa dakarun sojin ta su yi ruwa da tsaki wajen mu'amalantar harkokin ta na zabe, sai dai a wani sa'ilin hakan ya kasance muhimmiyar bukata duba da tabarbarewar al'amurra.

Dakarun Sojin Najeriya sun yi ruwa da tsaki wajen mu'amalantar harkokin babban zaben kasa na bana da ya gudana a sakamakon yadda al'amurra na siyasa suka rincabe tare da hauragiya ta a mutu ko a yi rai da ta mamaye zaben kasar nan.

Tsagerancin 'Yan siyasa ya sa Sojoji suka mu'amalanci zaben 2019 - Felix Omobude
Tsagerancin 'Yan siyasa ya sa Sojoji suka mu'amalanci zaben 2019 - Felix Omobude
Asali: Facebook

Ire-iren munanan ababe na ta'addanci ka ma daga zubar da jini da salwantar rayukan al'umma, kone kayayyakin zabe da kuma ofisoshin hukumar INEC tun gabanin zabe, ya sanya tilas rudunar dakarun sojin Najeriya ta mike tsaye domin kare martabar al'umma da kuma kasa baki daya.

Shugaban cibiyar Limaman addinin Kirista ta Pentecostal Fellowship, Rabaran Felix Omobude, shi ne ya yi tsokaci yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar Vanguard dangane da al'amurran da suka shafi zaben bana.

Sai dai a yayin kasancewar Soja ba bu wasa da Hausawa ke ma sa kirari na marmari daga nesa, Rabaran Omobude ya yi na'am da cewar ruwa da tsakin dakarun soji ya haifar da nakasu yayin zabuka musamman a bangaren yadda fargaba ta sanya al'umma suka gaza fitowa wajen kada kuri'un su.

KARANTA KUMA: Kalubalantar Sakamakon Zabe: Kotun daukaka kara za ta fara sauraron korafin Atiku a ranar Laraba

Rabaran Omobude ya yabawa rawar da dakarun sojin ta taka musamman sojin sama da na ruwa wajen jigila da rarraba kayayyakin zabe a yankunan da Motoci ba sa iya kai wa gare su. Ya kuma yabawa gudunmuwar dakarun sojin kasa wajen dakile satar akwatunan zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel