Kalubalantar Sakamakon Zabe: Kotun daukaka kara za ta fara sauraron korafin Atiku a ranar Laraba

Kalubalantar Sakamakon Zabe: Kotun daukaka kara za ta fara sauraron korafin Atiku a ranar Laraba

A ranar Laraba, kotun daukaka da ke zaman ta a garin Abuja za ta fara sauraron korafi na kalubalantar sakamakon zabe da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar ma ta.

Atiku Abubakar, da ya kasance tsohon mataimaikin shugaban kasar Najeriya, na ci gaba da rashin amincewa tare da kalubalantar sakamakon zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kalubalantar Sakamakon Zabe: Kotun daukaka kara za ta fara sauraron korafin Atiku a ranar Laraba
Kalubalantar Sakamakon Zabe: Kotun daukaka kara za ta fara sauraron korafin Atiku a ranar Laraba
Asali: Facebook

Atiku da jam'iyyar sa ta PDP na neman kotu ta yi watsi da hukuncin hukumar zabe watau INEC da ta kaddamar da shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar makonni kadan da suka gabata.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, manyan alkalai biyar na Kotun daukaka za su jagoranci zaman sauraroron korafin Atiku da na jam'iyyar sa ta PDP da suka gabatar gabanta tun a ranar 18 ga watan Maris.

KARANTA KUMA: Zargin ta'annati da dukiya yayin yakin zabe - Buhari da Atiku za su gurfana a ranar 7 ga watan Mayu

Sai dai ba bu tabbaci na yiwuwar shugabar Kotun, Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa za ta jagoranci zaman kotu ko kuma Mai shari'a Abdul Aboki da ya yanke hukuncin bai wa dukkanin 'yan takara damar gudanar da bincike kan kayayyakin da hukumar INEC ta ribata wajen gudanar da zabe.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, Atiku bayan gudanar da bincike ya na da cikakken yakinin cewa shi ya yi nasara a yayin zaben inda ya ke da tabbacin samun nasara da kimanin kuri'u 18,356,732 fiye da adadin kuri'u da Buhari ya samu na 16,741,430.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel