Kasafin Kudi: Ban ji dadin yadda Majalisar Saraki ta mu'amalanci gwamnati na ba - Buhari

Kasafin Kudi: Ban ji dadin yadda Majalisar Saraki ta mu'amalanci gwamnati na ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin sa gami da bacin rai dangane da wasu al'amurra da hukunce-hukuncen da Majalisar dattawa karkashin jagorancin Abubakar Bukola Saraki ta aiwatar a baya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya yi nadama gami da da na sanin yadda al'amurra suka gudana cikin zauren majalisar tarayya karkashin jagorancin Saraki da kuma kakakin majalisa, Yakubu Dogara wajen karkatar da akalar jagorancin kasar nan.

Kasafin Kudi: Ban ji dadin yadda Majalisar Saraki ta mu'amalanci gwamnati na ba - Buhari
Kasafin Kudi: Ban ji dadin yadda Majalisar Saraki ta mu'amalanci gwamnati na ba - Buhari
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya bayyana bacin ran sa da kuma bakin ciki yayin ganawa da zababbun 'yan Majalisar tarayya da kuma zababbun gwamnoni na jam'iyyar APC a wata Liyafar dare cikin fadar sa ta Villa a ranar Litinin da ta gabata.

Buhari musamman ya bayyana bacin ran sa dangane da yadda majalisar tarayya ta kawo tangarda da tsaikon shigar da kasafin kudin kasar nan na bara cikin dokar kasa da hakan ya dagwala al'amurran gwamnatin sa.

A sanadiyar haka shugaban kasa Buhari ya ke kalubalantar wadanda za su kasance a sabuwar Majalisar tarayya ta gwamnatin kasar nan da su sauya yanayi na gudanar da al'amurra sabanin na Majalisar baya domin tabbatuwar ci gaba a kasar nan.

KARANTA KUMA: Zargin Zamba: Kotu ta waiwayi surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo

Yayin kira na neman daura damara da zage dantse wajen sauke nauyin da rataya a wuyan su, Buhari ya tuni da cewar dole sai da hadin kansu zai cimma manufa ta kyakkyawar makoma da ya kudirta a Najeriya.

Cikin zayyana na sa jawaban, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya ce babbar manufa ta wannan taro ba ta wuce samar da hadin kai da kulla kyakkyawar alaka ta aminci tsakanin tsaffi da kuma sabbin Sanatoci domin kafa nagartaccen ginshiki tare da fadar shugaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel