Zargin Zamba: Kotu ta waiwayi surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo

Zargin Zamba: Kotu ta waiwayi surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo

A ranar Talata Mai shari'a Mojisola Dada, Alkalin Kotun laifuka na musamman ta Ikeja, ya shaidawa John Abebe, dan uwa ga Marigayiya mai dakin tsohon shugaban kasa, Stella Obasanjo, cewa akwai tuhuma ta zargin zamba da zai amsa.

Mai Shari'a Mojisola Dada, ya shaidawa John Abebe cewa, akwai tuhumar kotu ta zargin sa da aikata laifin zamba cikin aminci cikin wata takardar shaidar kwantiragin harkar man fetur da zai amsa.

Bayan da hukumar hana yiwa tattalin arziki ta'annati EFCC ta janye zargin ta daga kan Mista Abebe tun a ranar 19 ga watan Janairu, Alkali Dada ya ce kotu ta aminta da shaidun da hukumar EFCC ta gabatar a baya.

Zargin Zamba: Kotu ta waiwayi surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo
Zargin Zamba: Kotu ta waiwayi surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo
Asali: UGC

A yayin da Mista Abebe ke madogara da sashe na 239 sakin layi na 1 cikin tanadi na dokokin shari'ar kasar nan, Lauyan sa Uche Nwokedi, ya nemi kotu ta yi watsi da korafin da hukumar EFCC ta shigar sakamakon rashin gabatar da gamsasshiyar shaida.

Kotu ta gaza kama Mista Abebe da laifin zamba da ake zargin sa da aikatawa yayin zaman ta da aka gudanar a ranar 26 ga watan Yulin 2018. Hukumar EFCC ta ce Mista Abebe ya aikata laifin a ranar 22 ga watan Yunin 2010.

Hukumar EFCC ta shimfida zargi na tuhumar Mista Abebe a sakamakon yadda ya ƙirƙiri wata wasika ta kamfanin BP Exploration Nig. Ltd. da kwanan wata na ranar 30, Nuwamban 1995 zuwa ga kamfanin Inducon (Nig.)Ltd.

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya godewa al'ummar jihar Kano da suka sake zaben sa

Cikin wasikar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Mista Abebe ya yi kagen harkar cinikayyar ma'adanan man fetur ta kimanin Dalar Amurka Miliyan hudu da ya sabawa sashe na 120 da kuma na 126 cikin dokokin miyagun laifuka na jihar Legas da aka tanada a shekarar 2003.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu Alkali Dada ya ce dole Mista Abebe ya wanke kansa sakamakn wannan sahihin zargi da hukumar EFCC ta rataya a wuyansa. Ya daga sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Yunin 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel