Gwamna Ganduje ya godewa al'ummar jihar Kano da suka sake zaben sa

Gwamna Ganduje ya godewa al'ummar jihar Kano da suka sake zaben sa

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi furuci godiya da kuma jinjina ga daukacin al'ummar jihar Kano da suka sake zaben sa a matsayin gwamnan jihar karo na biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, a ranar Lahadin karshen makon da ya gabata ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin wanda ya lashe karashen zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Yayin karashen zabe na cike gurbi da aka gudanar a kananan hukumomi 28 cikin 44 na jihar Kano, Gwamna Ganduje ya nasara da kimanin kuri'u 45,875, inda ya lallasa babban abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf wanda ya samu kuri'u 10,239 kacal.

Gwamna Ganduje ya godewa al'ummar jihar Kano da suka sake zaben sa
Gwamna Ganduje ya godewa al'ummar jihar Kano da suka sake zaben sa
Asali: UGC

Babban Baturen zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Bello Shehu, yayin bayyana sakamakon zabe a ranar Lahadi ya ce, gwamna Ganduje ya samu gamayyar kuri'u 1,033,695 yayin da Abba Yusuf ya samu kuri'u 1,024,713.

Gwamna Ganduje wanda ya sha alwashi yayin gabatar da jawaban sa na samun nasara a daren Lahadi cikin birnin Kano, ya yi kira na neman goyon bayan dukkanin al'ummar jihar baki daya domin tabbatar da kyakkyawar makoma ta inganta ci gaban ta da kuma aminci.

Ya kuma bayyana cewa sabuwar gwamnatin sa za ta sauya salo tare da shimfida kayattaccen tsari na sanya kowa a tafiyar sa duk da sabani na akidar siyasa wajen karkatar da akalar sa ta jagoranci domin fidda jihar Kano zuwa tudun tsira.

KARANTA KUMA: Karashen zabe: Kungiyar EU ta yaba da kwazon hukumar INEC

Ba ya ga mika godiya ga al'ummar jihar Kano da suka sanya aminci a jagorancin sa da kuma hadin kai da suka bayar wajen tabbatar da nagartaccen zabe cikin lumana da kwanciyar hankali a ranar 23 ga watan Maris, ya sha alwashin cewa wadanda suka kada ma sa kuri'a ba za su yi da na sani ba.

Gwamna Ganduje da ake yiwa lakabi da Khadimul Islama, ya sha alwashin kammala duk wasu ayyuka da gwamnatin sa ta farar tare da dashen sabbi musamman a bangaren inganta harkokin kiwon lafiya, noma, ilimi, tallafin Mata da Matasa, da kuma uwa uba ingancin tsaro domin wanzar da zaman lafiya.

Ya kuma yabawa kwazon hukumar INEC da ta haskaka kwarewar ta yayin gudanar da zaben kasa. Ya yi jinjina ga daukacin al'ummar Najeriya da suka tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hanyar kada ma sa kuri'u yayin a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel