Karashen zabe: Kungiyar EU ta yaba da kwazon hukumar INEC

Karashen zabe: Kungiyar EU ta yaba da kwazon hukumar INEC

Kungiyar Tarayyar Turai EU (European Union), reshen sanya idanu a kan babban zabe na Najeriya, ta yaba da kwazon hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC dangane da inganta harkokin ta na gudanarwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kungiyar EU reshen sa ido kan babban zabe na Najeriya, ta yabawa kwazon hukumar INEC sakamakon inganta harkokin ta na gudanarwa yayin karashin zaben wasu gwamnoni da ya wakana a ranar 23 ga watan Maris.

Karashen zabe: Kungiyar EU ta yaba da kwazon hukumar INEC
Karashen zabe: Kungiyar EU ta yaba da kwazon hukumar INEC
Asali: UGC

Cikin wata sanarwa da ta gabatar a ranar Litinin, kungiyar EU ta bayyana lurar ta akan yadda hukumar zabe ta inganta harkokin gudanarwa yayin zaben daki-daki cikin aminci da kuma tsari kamar yadda ta shimfida.

EU ta yabawa hukumar INEC musamman yadda ta ribaci na'urar tantance masu zabe a kowace rumfar zabe tare da kammala tattara sakamakon zaben cikin sa'o'i 24 kamar yadda ta yi tanadi a mafi akasarin jihohin kasar nan da ta aiwatar da karashen zabe.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada Jauro sabon shugaban NESREA

Jagoran masu sanya idanu, Maria Arena, ta fayyace yadda hukumar INEC ta kammala tattara sakamakon karashen zaben jihohin Bauchi, Benuwai, Filato da kuma Sakkwato cikin sa'o'i 24 in ban da jihar Kano ta aka samu akasi a sakamakon dalilai na rashin tsaro.

A yayin da kungiyar za ta bayar da cikakken rahoto na diddigi a watan Yuni, Misis Arena ta ce zai hadar da shawarwari akan yadda hukumar INEC za ta kara kaimi wajen inganta harkokin zabe a lokuta na gaba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel