Buhari yana kasa rijiyoyin man Najeriya ga daidaikun mutane - Falana

Buhari yana kasa rijiyoyin man Najeriya ga daidaikun mutane - Falana

Babban Lauyan nan na Najeriya watau Femi Falana yayi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta daina raba rijiyoyin mai ga wasu tsirarrun mutane ko kuma yayi wuf ya dauki mataki.

Wannan Lauya mai fafutukar kare hakkin jama’a a Najeriya ya zargi shugaba Buhari da kasa rijiyoyin man kasar nan ga wasu mutane da kuma wasu kamfanonin kasashen waje. Lauyan yake nuna cewa zai je kotu a kan hakan.

Femi Falana SAN yayi wannan bayani ne a wata wasika ta musamman da ya rubuta mai taken ‘Request To Stop Allocating Oil Blocks To Private Individuals And Corporate Bodies’ a Ranar Asabar 23 ga Watan Maris dinnanmai-ci.

KU KARANTA: Kila a sake maka Babban Alkalin Najeriya a Kotun Najeriya

Buhari yana kasa rijiyoyin man Najeriya ga daidaikun mutane - Falana
Lauya Falana ya nemi Buhari ya daina raba rijiyoyin man Najeriya
Asali: UGC

Falana yace wannan abu da shugaban kasa Buhari yake yi ya sabawa sahse na 16(2)(C) na kundin tsarin mulkin Najeriya. Dokar kasa ta haramta a kyale dukiyar al’umma ta rika yawo tsakanin wasu gungun mutane daidaiku a Najeriya.

Lauyan ya kuma cewa wannan rabon arzikin Najeriya da shugaba Buhari yake yi, ya zama ana fifita wasu a kan wasu ‘yan kasar. A tsarin mulkin Najeriya, kowa yana damar cin arzikin kasar nan ba tare da nuna wani banbanci ba.

Wannan rikakken Lauya ya kuma kawo wasu sashe na dokokin Najeriya da su ka haramtawa shugaban kasar zaben wasu masu fuska da mai, a rika ba su kyautar rijiyoyin man fetur don haka yace idan ba a gyara ba zai dauki mataki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel