Yanzu-yanzu: An soke zaben gwamnan jihar Zamfara tare dana sauran 'yan majalisun jihar da suke jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: An soke zaben gwamnan jihar Zamfara tare dana sauran 'yan majalisun jihar da suke jam'iyyar APC

- Wata kotun daukaka kara ta soke zaben da aka yi na gwamna a jihar Zamfara

- Ba a nan abin ya tsaya ba, kotun ta kuma soke zaben 'yan majalisun jiha dake jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: An sauke sabon gwamnan jihar Zamfara tare da mukarrabansa na jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: An sauke sabon gwamnan jihar Zamfara tare da mukarrabansa na jam'iyyar APC
Asali: Facebook

A jiya ne, jam'iyyar APC mai mulki ta samu wani koma baya, yayinda wata Kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta ki amincewa da sakamakon zaben fidda gwani da aka yi a jihar Zamfara, tun daga kan gwamna har 'yan majalisun jihar.

A zaben da ya gabata na fidda gwani a jihar ta Zamfara, an dan samu rudani a jam'iyyar ta APC, inda aka je matsayin da kotu ta kori dukkan 'yan takarar gwamnan dake jam'iyyar ta APC

Sai dai kuma wata kotu a jihar ta Zamfara ta nuna amincewar ta, inda ta bukaci hukumar zabe ta kasa data yi amfani da 'yan takarar da jam'iyyar ke dasu a kasa.

Sai dai kuma daya daga cikin Sanatocin jihar, Sanata Kabiru Marafa, ya nuna rashin amincewarshi dangane da hukuncin da kotun jihar ta bayar, indayace kotun bata da wani dalili na yanke hukunci.

A bayanin da alkalin kotun yayi, ya bayyana cewa kotu zata yanke hukunci mai tsauri, yadda hakan zai zama darasi ga 'yan siyasar kasar nan.

KU KARANTA: PDP zata ja daga idan ba'a baiwa Abba Kabir Gwamnan jihar Kano ba

Shi kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya bukaci hukumar zabe ta kasa data baiwa, dan takarar gwamnan jihar ta Zamfara takardar shaidar zama gwamnan jihar.

Sannan kuma ya yiwa dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP murna, akan lashe zaben da yayi. Sannan ya jinjinawa Sanata Kabiru Marafa, akan irin namijin kokarin da yayi, duk da cewa kuwa shi dan jam'iyyar APC ne, amma bai bari anyi magudi akan idon shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel