Kwankwaso da PDP ne su ka haddasa rigima lokacin zaben gwamna a Kano - BMO

Kwankwaso da PDP ne su ka haddasa rigima lokacin zaben gwamna a Kano - BMO

Kungiyar kare manufofin shugaba Buhari (BMO) ta zargi jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan jihar Kano kuma madugun kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da ingiza wutar rigingimu a Kano bayan an bayyana cewar gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben gwamnan jihar.

A wani jawabi da shugaban BMO, Niyi Akisiju, da sakataren sa, Cassidy Madueke, su ka fitar a Abuja sun bayyana cewar tuni dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya kyara wa magoya bayansa su tayar da rikici ta hanyar furta cewar za a samu barkewar rigima matukar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar APC ta lashe zaben gwamnan Kano.

BMO ta kara da cewar babu wanda ya fi dace wa a dora wa alhakin barkewar rikici lokacin zabe da kuma bayan sanar da sakamako sai jam'iyyar PDP da darikar Kwankwasiyya.

Kungiyar ta ce PDP da Kwankwasiyya sun dauki nauyin yada karya da farfaganda a lokacin da ko kammala kada kuri'u ba a yi ba. BMO ta kara da cewa yin hakan ya kara tunzura jama'a da su ka dauki cewar labaran da su ka karanta a dandalin sada zumunta gaskiya ne.

Kwankwaso da PDP ne su ka haddasa rigima lokacin zaben gwamna a Kano - BMO
Kwankwaso
Asali: Depositphotos

"Sun yada hotunan tashin hankali na wasu kasashe daban da sunan a jihar Kano abin ya faru. Daya daga cikin irin hotunan da su ka yi amfani da su an gano cewar na wani rikici ne da ya faru a wata mashaya a kasar Ghana.

"Sannan sun kara dauko wasu hotunan daga rigingimun jihar Filato su na yada wa duk don su nuna cewar ba a gudanar da zabe cikin zaman lafiya ba a jihar Kano bayan ba haka zancen yake ba," a cewar BMO.

DUBA WANNAN: Mukami daya kacal zamu bar wa PDP a majalisa - Oshiomhole

Sannan su ka cigaba da cewa, "babu abinda ya girgiza fiye da yadda mu ka ga babban dan siyasa kamar Kwankwaso wanda ya rike mukamin gwamna, ministan tsaro da kuma neman takarar shugaban kasa amma yana rura wutar rikici.

"Hatta a lokacin da ake tsaka da kada kuri'a bai sassauta da fitar da kalaman tashin hankali ba kamar yadda mu ka gani a tattaunawar sa da gidan Talabijin na Channels kuma tun kafin kowa ya ji lokacin da yake furta cewar babu yadda za a yi jam'iyyar PDP ta fadi zaben gwamna a Kano."

Kazalika, BMO ta yabi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, bisa halin dattako da ya nuna a lokacin da ake gudanar da zaben gwamna a Sokoto duk da yana fuskantar barazanar faduwar zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel