Da dumin sa: An shiga ganawar sirri tsakanin shugaba Buhari da Sanatocin APC

Da dumin sa: An shiga ganawar sirri tsakanin shugaba Buhari da Sanatocin APC

A daren nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanatocin jam'iyyar APC su ka shiga wata ganawar sirri a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Sanatocin da suka halarci ganawar sun hada da sabbi da tsofin sanatocin da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Bayan sanatocin, rahotanni sun bayyana cewar akwai wasu gwamnoni da suka halarci taron. Daga cikin gwamnonin da aka hango a fadar shugaban kasan akwai na jihar; Legas, Filato, Kogi, Kaduna, Jigawa, Kebbi, Zamfara da Osun.

Kazalika, akwai shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a wurin taron.

Shugaba Buhari ya karbi bakin na sa a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa, inda za su ci abincin dare tare.

Da dumin sa: An shiga ganawar sirri tsakanin shugaba Buhari da Sanatocin APC
Sanatocin APC yayin wata ziyara ga Buhari
Asali: Facebook

Batun rabon mukami da zaben shugabannin majalisa ne zai mamaye tattaunawar da za a yi tsakanin shugaba Buhari da bakin na sa.

DUBA WANNAN: Mukami daya kacal zamu bar wa PDP a majalisa - Oshiomhole

Sabanin shekarar 2015 da shugabancin majalisar dattijai ya fada tsagin sanatocin APC da ba sa ga maciji da fadar shugaban kasa da shugabancin jam'iyya, a wannan karon APC ta tsaya kai da kafa wajen ganin mambobin da ke biyayya ga shugabancin jam'iyya da fadar shugaban kasa.

Taron da aka fara da misalin karfe 8:00 na daren nan, har yanzu ba a kammala shi ba lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Daga cikin sanatocin da ke harin kujerar shugaban majalisar dattijai akwai sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe, sanata Ali Ndume daga jihar Borno da sanata Danjuma Goje daga jihar Gombe da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel