Mutane 32 sun sace sama da tiriliyan 1.3 karkashin Jonathan - Ibrahim Magu

Mutane 32 sun sace sama da tiriliyan 1.3 karkashin Jonathan - Ibrahim Magu

Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC< Ibrahim Magu, ya bayyana cewa an sace akalla kudi tiriliyan 1.3 tsakanin shekarar 2011 da 2015 karkashin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Magu ya bayyana cewa a cikin wadannan shekaru, mutane 32 suka talauta Najeriya karkashin Jonathan.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wani taron da cibiyar saye-sayen kayan gwamnati wato Bureau of Public Procurement a ranar Litinin, 25 ga watan Maris, 2019.

A jawabin da Sakataren EFCC, Ola Olukayode, ya gabatar a madadin Magu, ya bayyana irin abubuwan da Najeriya zata amfana da irin makudan da kudin mutanen nan suka handama.

Yace: "Kashi daya cikin ukun kudin nan, za'a iya gina hanyoyin kilomita 500, za'a makarantu 200, za'a ilmantar da yara 4000 daga matsayin firamre zuwa jami'a idan aka rabawa kowannesu N25m; za'a iya gina gidaje masu dakuna biyu 20,000 a fadin tarayya kuma fiye da haka.

"Amma da irin wannan sata, ba za'a iya gina wadannan hanyoyi, makarantu, da gidaje ba, kuma wadannan yara ba zasu taba samun irin wannan ingantaccen ilimi ba saboda rub da cikin da wasu yan kalilan sukayi domin kansu da iyalansu."

KU KARANTA: Shikenan: Buhari ya zabi Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila matsayin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai

Ya kara da cewa yadda ake siyan kayayyakin gwamnatin a Najeriya na daga cikin manyan dalilan da yasa rashawa ke cigaba da gudana a ma'aikatun gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel