Watakila Gwamnatin Buhari ta jibgo wasu sababban laifuffuka a kan CJN

Watakila Gwamnatin Buhari ta jibgo wasu sababban laifuffuka a kan CJN

Labari ya iso mana daga Jaridar Sahara Reporters cewa ana shirin sake maka babban Alkalin Najeriya, Walter Onnoghen, da aka dakatar daga kan kujerar sa da wasu sababbin laifi a gaban kotu.

Wani jami’on gwamnatin tarayya ya bayyanawa jaridar cewa ana shirin sake jibgawa Walter Onnoghen wasu tarin zargin laifi a kan wadanda ke wuyan sa yanzu haka. Yanzu haka Onnoghen yana fuskantar shari’a a gaban kotun CCT.

Majiyar ta bayyanawa Sahara Reporters cewa ko da mai shari’a Walter Onnoghen ya tsallake zargin da ke kan sa a gaban Alkalan CCT mai binciken kadarorin ma’aikatan Najeriya, za a kuma daura wasu laifi na dabam a kan wuyan sa.

Jaridar ta samu wannan labari ne a Ranar Lahadin da ta gabata ta bakin wani da ba zai so a bayyan sunan sa a fili ba. Wannan babban jami’in na gwamnatin tarayya yace za a kai Alkali Walter Onnoghen ne gaban wani kotun tarayya.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta na nema a cafko mata Ayo Oke da Mai dakin sa

Watakila Gwamnatin Buhari ta jibgo wasu sababban laifuffuka a kan CJN
GwamnatinTarayya za ta bi Babban Alkalin Najeriya da wasu laifuka
Asali: Twitter

Laifin da ke kan Alkali mai shari’an a yanzu shi ne kin bayyana kadarorin da ya mallaka bayan ya shiga ofis. Wannan ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige sa daga kan mukamin say a kuma nada wani Mukadasshin CJN a kasar.

Haka zalika majalisar shari’a ta Najeriya NJC tana binciken wasu makudan kudin kasar waje da aka samu a cikin asusun babban Alkalin kasar. Kawo yanzu dai ana cigaba da gudanar da binciken da ake sa rai za a fitar da rahoto nan gaba.

Yanzu kuma akwai yiwuwar a taso sa gaba da laifin rashin biyan haraji, da karbar cin hanci da rashawa da kuma safarar makudan kudi wanda ya sabawa doka a lokacin yana kan kujerar Alkalin Alkalai na CJN.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel