Shikenan: Buhari ya zabi Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila matsayin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai

Shikenan: Buhari ya zabi Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila matsayin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ra'ayinsa kan Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa, da Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai a zaben majalisar dokokin da za'a gudanar a watan Yuni. Cable ta bada rahoto.

Kwamitin gudanarwan jam'iyyar APC ta shiga ganawa da zababbun mambobin majalisar wakilan tarayya ranar Litnin, 25 ga watan Maris, 2019.

Lawan da Gbajabiamila wadanda sune shugabannin masu rinjaye a majalisar dattawa da wakila na yanzu, sun samu goyon bayan shugaba Buhari a 2015 amma shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisa Yakubu Dogara, sun hada kai da wasu yan PDP domin kawar dasu.

KU KARANTA: Rahoto: Shanaye 31 sun bace a ofishin yan sanda

Yayinda Ahmed Lawan ya ki halartan taro zaben, Gbajabiamila ya sha kasa a hannun Dogara da kuri'u takwas.

Amma a yanzu, Saraki ya fadi warwas yayinda dan takaran APC ya dokesa a zaben kujerar mazabar Kwara ta tsakiya yayinda shi kuma Dogara zai dawo majalisar amma yan PDP basu da yawan zabensa,

A majalisar dattawa, jam'iyyar APC na da mambobi 65, jam'iyyar PDP na da 40. A majalisar wakilai kuma, jam'iyyar APC ta ninka PDP wajen yawan mambobi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel