Mutane 32 sun sace fiye N1.3tn a cikin shekara hudu - Magu

Mutane 32 sun sace fiye N1.3tn a cikin shekara hudu - Magu

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya bayyana cewar mutane 32 sun sace fiye da tiriliyan N1.3 a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Magu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a wurin bayar da horo ga ma'aikatan hukumomin gwamnati da ma'aikatu da cibiyar 'Bureau of Public Procurement (BPP) ta gudanar yau, 25 ga watan Maris, a garin Legas.

A wata takarda da Ola Olukoyede, sakataren hukumar EFCC, ya karanta a madadinsa, Magu ya koka a kan yadda Najeriya ke asarar kudade sanadiyar cin hanci da wasoso a kan dukiyar gwamnati, kudaden da ya ce sun isa a gina hanyoyi, makarantu da asibitoci da dukkan 'yan kasa zasu mora.

Mutane 32 sun sace fiye N1.3tn a cikin shekara hudu - Magu
Ibrahim Magu
Asali: UGC

"Irin wannan mummunar sata ce ta hana a gina hanyoyi, makarantu da asibitoci da dukkan 'yan kasa zasu amfana. Wasu 'yan tsirarun mutane sun kawashe kudaden, sun hana 'ya'yan talaka samun ilimi mai nagarta da samun nagartattun asibitoci da sauran su," a cewar Magu.

Ya kara da cewa cin hanci ya samu gindin zama a hukumomin gwamnati ne ta hanyar bayar da kwangila da sayen kayen amfanin gwamnati ko ma'aikata.

DUBA WANNAN: Mukami daya kacal zamu bar wa PDP a majalisa - Oshiomhole

Daga cikin hanyoyin da Magu ya lissafa cewar hukumomi na amfani da su wajen kwasar kudin gwamnati akwai karbar nagoro daga hannun 'yan kwangila, bayar da kwangila ga abokai ko 'yan uwa, kin bin ka'ida wajen zaben kamfanin da ya dace a bawa kwangila, kara kudin kwangila da gan-gan da sauran su.

Magu ya bayyana cewar har yanzu akwai ma'aikatan gwamnati ma su gaskiya da ke kwatanta gaskiya a duk inda aiki ya kai su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel