Rahoto: Shanaye 31 sun bace a ofishin yan sanda

Rahoto: Shanaye 31 sun bace a ofishin yan sanda

Wasu yan kabilar Fulani dake kauyen Kaban, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i da kwamishanan yan sandan jihar, Ahmad AbdulRahman, da su taimaka musu wajen kwato shanayensu dake hannun yan sanda.

Yan Fulanin sun bayyana cewa shanaye 31 da tinkiyoyi 2 sun bace bayan da jami'an yan sanda suka kawo hari kauyensu.

Daya daga cikin yan Fulanin mai suna, Abubakar Ibrahim, ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa tun lokacin da tawagar yan sandan suka kai farmaki, basu samu amso shanayensu ba.

Abubakar wanda akafi sani da Habu, ya bayyana cewa sun kashe kudi kimanin 1.750 million domin a dawo musu da shanayensu amma har yanzu babu labari.

"Dan uwana da sirikina da suka je tambayan shanayen a ofishin yan sanda, an garkamesu na tsawon makonni biyu. Sai da muka karbi belinsu da kudi N580,000.

"Kawo yanzu, mun kashe N1.75 miliyan domin amso shanayenmu da tinkiyoyi amma yan sanda sun cigaba da karban kudadenmu ba tare da fada mana inda suke ba. Hafsan dan sanda kulli yaumin fada mana yake an kai shanayenmu Abuja.

"Wannan shine dalilin da yasa muke kira ga gwamnan jihar Kaduna da kwamishanan yan sanda su sanya baki ta hanyar yiwa yan sandan magana su dawo mana da shanayenmu."

KU KARANTA: An cigaba da tattara zaben Tabawa Balewa a jihar Bauchi

Habu ya bayyana cewa dalilin da yasa suka kwashe shanayen a karon farko shine suna zarginsa da mallakar bindiga. Ya musanta wannan zargi kuma ya ce bai taba mallakar bindiga ba a rayuwarsa.

Mai anguwa garin Kaban, Alhaji Shehu Muhammad, ya tabbatar hakan kuma ya bayyana cewa mutanen gidansu Habu masu son zaman lafiya ne. Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar, Yakubu Sabo, ya ki magana a kan al'amarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel