Mukami daya kacal zamu bar wa PDP a majalisa - Oshiomhole

Mukami daya kacal zamu bar wa PDP a majalisa - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewar mambobin jam'iyyar sa ne kadai zasu samu mukami a majalisar tarayya in banda kujerar shugaban marasa rinjaye.

Da yake magana yayin wata ganawa da mambobin majalisar wakilai da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar APC, Oshiomhole ya ce APC zata yi amfani da rinjayen da take da shi wajen zabar shugabannin majalisar.

Oshiomhole ya kara da cewar mambobin jam'iyyar APC ne zasu shugabanci kwamitocin majalisar in banda shugabancin kwamitin asusun jama'a, wanda doka ta bayyana cewar na jam'iyyar adawa ne.

An gudanar da taron ne a cibiyar Yar'Adua da ke Abuja, birnin tarayya.

Mukami daya kacal zamu bar wa PDP a majalisa - Oshiomhole
Oshiomhole
Asali: Twitter

"Muna da yawan mambobin da zamu samar da kakakin majalisa, a saboda haka shugaban majalisa dole ya kasance dan jam'iyyar APC.

"Ina son ku saka a cikin zukatan ku cewar tamkar 'yan uwan juna mu ke, za mu hada kai kamar yadda alamar tsintsiya ta jam'iyyar mu ke nunua wa.

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Kwamitin kamfen din Buhari ya kai karar PDP wurin rundunar 'yan sanda da DSS

"Mu na da yawan zamu karbi shugabancin majalisa kuma zamu yi amfani da yawan mu don cimma wannan buri na mu.

"Kujerar shugabanci daya ce APC za ta bari; kujerar shugaban marasa rinjaye. Ba zamu raba mukamin shugabancin majalisa da na kwamitoci da wata jm'iyyar ba. Da 'yan Najeriya a son wata jam'iyya ta shugabanci majalisa da sun zabi mambobin jam'iyyar fiye da na jam'iyyar APC," a cewar Oshiomhole.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel