Yanzu-yanzu: An cigaba da tattara zaben Tabawa Balewa a jihar Bauchi

Yanzu-yanzu: An cigaba da tattara zaben Tabawa Balewa a jihar Bauchi

An cigaba da tattaro sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa a ofishin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta a jihar Bauchi.

Ana cigaba da tattara sakamakon ne karkashin sabon baturen zaben, Dakta Musa Dahiru bisa ga hukumar INEC na cewa an cire tsohon baturen zaben, Misis Dominion Anosike, wacce ta rubuta wasikar cewa rayuwarta na cikin hadari.

Shugaban hukumar INEC na jihar Bauchi, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa sakamakon Tafawa Balewa da aka sace, an samoshi kuma za'a mikawa baturen zaben.

"Abinda sukeyi yanzu shine mika sakamakon zaben da sace daga unguwanni zuwa mattatarar zaben karamar hukua. Bayan haka mai tattara zaben a karamar hukuma zai kaiwa mai tattarawa na jiha sannan a sanar da zakara."

Ya kara da cewa: "Sashe 6 da 7 na dokar gudanar da zaben 2019 ya tanadi cewa muddin akwai rikici kuma aka sace sakamakon zabe ko aka yaga, mai tattara zabe yayi amfani da sauran takardun da ke hannunsa tare da umurnin shugaban hukumar na jiha."

"A yanzu haka, na bada umurnin nemo sakamakon kuma an samu, a yanzu haka masu tattara zabe a unguwanni suna gabatarwa ga mai tattara zaben karamar hukuma, wanda a karshe zai gabatarwa mai tattara zaben jihar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel