Sakamakon zabe: Kwamitin kamfen din Buhari sun kai karar PDP wurin rundunar 'yan sanda da DSS

Sakamakon zabe: Kwamitin kamfen din Buhari sun kai karar PDP wurin rundunar 'yan sanda da DSS

Kwamitin yakin neman zaben shugabn kasa Muhammadu Buhari a karkashin inuwar jam'iyyar APC ya zargi jam'iyyar hamayya, PDP, da satar hanya ta na'ura mai kwakwalwa domin leka bayanan sirri na hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC).

Kakakin kwamitin, Festus Keyamo, ya bayyana hakan a cikin wata takardar korafi da ya aike zuwa babban sifeton rundunar 'yan sanda da babban darektan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Bayanan dake cikin babbar na'ura mai kwakwalwa ta hukumar INEC na daga cikin manyan hujjoji da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ke kafa hujja da su a karar da ya shigar gaban kotu domin kalubalantar nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya bayyana cewar bayanan daga daga na'urar hukumar zabe ta kasa (INEC) sun nuna yadda aka rage ma sa kuri'u a zaben shugaban kasa a jihohi 31 da birnin tarayya, Abuja.

Sakamakon zabe: Kwamitin kamfen din Buhari sun kai karar PDP wurin rundunar 'yan sanda da DSS
Festus Keyamo
Asali: Depositphotos

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin takardar karar da ya shigar gaban koton sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaban kasa.

Dan takara na PDP ya bayyana cewar ya kayar da shugaba Buhari da tazarar kuri'u 1,615,302.

Ya ce na'urar hukumar INEC ta nuna cewar ya samu adadin kuri'u 18,356,732 da suka bashi rinjaye a kan shugaba Buhari, wanda ya samu kuri'u 16,741,430.

Atiku ya yi ikirarin cewar bayanan da ke kan na'urar INEC sun tabbatar da cewar shine ya lashe zaben kujerar shugaban kasa amma INEC ta bayyana sunan shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Yadda APC tayi amfani da sojoji wajen tafka magudi - Buba Galadima

Wadannan kalamai da Atiku da PDP ke yi ne ya sa Keyamo ya aike da takardar korafi zuwa hukumomin tsaro bisa zargin PDP da bin haramtattun hanyoyi domin yiwa INEC leken asiri a na'urar su ta tattara bayanai.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

A sanarwar INEC ta bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 yayin da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 11,262,978.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel