Kotu ta daga sauraron karar El-Zakzaky har sai baba-ta-gani

Kotu ta daga sauraron karar El-Zakzaky har sai baba-ta-gani

Wata babbar kotun jihar Kaduna karkashin mai shari'a Gideon Kurada ta daga sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da shugaban kungiyar mabiya shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, har sai baba-ta-gani.

Alkalin kotun ya bayyana cewar ya daga sauraron karar ne ba tare da saka ranar dawowa ba saboda nadin da aka yi ma sa a matsayin alkali a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya.

Tun a shekarar 2015 gwamnati ta kama El-Zakzaky tare da matar sa, Zeenat, biyo bayan wata kazamar arangama tsakanin mabiyansa da dakarun sojin Najeria a garin Zaria dake jihar Kaduna.

Rahotann sun bayyana cewar an kashe mabiya shi'a kimanin su 300 yayin artabu da dakarun sojin.

Ana tuhumar El-Zakzaky da matar sa da hada baki domin aikata kisa, taro ba bisa ka'ida ba, da tayar da tsugune tsaye da sauran su.

Kotu ta daga sauraron karar El-Zakzaky har sai baba-ta-gani
El-Zakzaky
Asali: Facebook

Da yake gana wa da manema labarai bayan yanke hukuncin kotun, Femi Falana, lauyan dake kare wadanda ake tuhuma, ya ce wadanda yake karewa basu samu damar bayyana a gaban kotu ba saboda yanayin rashin koshin lafiya da su ke ciki.

Ya ce tun ranar 14 g watan Disamba na shekarar 2015 da aka rufe su, ba a bawa lafiyar su kulawa ba, tare da bayyana cewar su na matukar bukatar a duba lafiyar su.

DUBA WANNAN: Zagaye na biyu: INEC za ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Bauchi a yau

"Kotu ta daga sauraron karar su har sai baba ta-gani a daidai lokacin da su ke cikin tsananin bukatar a duba lafiyar su," a cewar Falana.

A ranar 22 ga watan Janairu na shekarar 2019 ne Jastis Kurada ya bawa gwamnatin Kaduna umarnin ta bawa El-Zakzaky da matar sa dama don a duba lafiyar su, umarnin da Falana ya ce gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel