Ina fatan mata su zamo kaso 41 na majalisar mijina — Aisha Buhari

Ina fatan mata su zamo kaso 41 na majalisar mijina — Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta ce tana fatan mata da yawa su kasance a majalisan mijinta kamar yanda shirin bayar da tallafi na Tony Elumelu (TEEP), ya kasance a 2019.

Yayinda take jawabin bude taro a shirin gidauniyar Tony Elumelu, Uwargidan shugaban kasar tace ta gode wa kokarin shirin wajen tabbatar da hallaran mata da dama.

Ta ce: “dabaran shigar da ofishin matar shugaban kasa a shirin shine, don kokarin ganin an kawo karshen mutuwar masu ciki, mutuwar jarirai da kananan yara ta hanyar bayar da tallafi domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban Najeriya.

Ina fatan mata su zamo kaso 41 na majalisar mijina — Aisha Buhari
Ina fatan mata su zamo kaso 41 na majalisar mijina — Aisha Buhari
Asali: UGC

“Cigaban mata wajen bada gudumuwa a fannin cigaban tattalin arziki wanda ya kasance alkhairi ga Gwamnatin Tarayya ta hanyoyi da dama.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Wani ginin ya sake rusowa a Lagas

“Mata suna cigaba da nuna kwarewarsu a cikin al’umma a fanni daban-daban, har da wuraren da maza suka fi yawa.

“Zamu so yin amfani da wannan daman don karfafa matan Najeriya, musamman daga Arewa, da su nemi shiga cikin shirin TEEP.”

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kwamitin bayar da shawara a kan yadda za a fara biyan sabon karin albashi da majalisa ta amince da shi.

Kwamitin ya mika rahoton ga shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja. A ranar 9 watan Janairu ne shugaba Buhari ya kafa kwamitin karkashin jagorancin masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, bayan jaddada aniyar sa ta kara ma fi karancin albashin ma'aikata.

Shugaba Buhari ya fara bayyana niyyar sa ta yin karin albashi a watan Disamba na shekarar 2018 yayin gabatar da kasafin kudi a gaban mambobin majalisar tarayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel