IGP ya bada umurnin binciken gaggawa kan lamarin kashe jami’in Civil Defence

IGP ya bada umurnin binciken gaggawa kan lamarin kashe jami’in Civil Defence

Sufeto Janar na yan Sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin gaggawa wajen binciken lamarin da yayi sanadiyyar kashe jami’in Civil Defence.

Jami’in mai suna Ogar Jumbo, ya mutu ne sakamakon duka da aka yi masa a ranar Laraba a Abuja a gaban matarsa da yaransa akan laifin kin bin dokan hanya.

Kwamishinan yan sanda birnin tarayya, Bala Ciroma, yayinda ya kai ziyarar jaje ga iyalan jami’in a wannan makon, yace rundunan yan sanda ta karbi laifin kisar killan da aka yiwa Mista Jumbo.

IGP ya bada umurnin binciken gaggawa kan lamarin kashe jami’in Civil Defence
IGP ya bada umurnin binciken gaggawa kan lamarin kashe jami’in Civil Defence
Asali: UGC

Shugaban rundunan yan sanda, Mista Adamu, yayi jaje ga Shugaban hukumar Civil Defence na kasa, abokai da yan uwan jami’in da aka kashe, ya kuma tabbatar da cewa za ayi matukar kokari don ganin an yanke hukuncin da ya dace a lamarin."

KU KARANTA KUMA: Wamakko da Ahmed Aliyu sun musanta kiran Gwamna Tambuwal a waya

Mista Adamu bada jawabin ne a ranar Asabar ta hannun kakakin rundunar, Frank Mba.

Shugaban yan sandan ya kuma bukaci hukumar NSCDC da iyalen jami’in da su zabi likita da zai shaidi gwaje-gwaje da za a gudanar a jikin gawan mamacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel