Zagaye na biyu: INEC za ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Bauchi a yau

Zagaye na biyu: INEC za ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Bauchi a yau

Labarin da Legit.ng ke samu yanzu haka na nuni da cewar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta kammala shiri tsaf domin cigaba da tattara sakamakon zaben raba gardama na gwamnam jihar Bauchi a yau, Litinin.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar INEC za ta cigaba da tattara sakamakon raba gardama da ka maimaita a karamar hukumar Tafawa Balewa da misalin karfe 4:00 na yamma a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Bauchi.

Cigaba da tattara sakamakon zabe na zuwa ne bayan wata kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bukatar dakatar da INEC daga cigaba da tattara wa da sanar da sakamakon zaben da aka maimaita a jihar Bauchi. Alkalin kotun, Jastis Inyang Ekwo, ya zartar da hukuncin ne a ranar Litinin (yau).

Da yake yanke hukunci a kan zaben, Jastis Inyang, ya bayyana cewar kotu ba ta da hurumin shiga maganar gaba daya.

Zagaye na biyu: INEC za ta cigaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Bauchi a yau
Cibiyar tattara sakamakon zaben Bauchi
Asali: UGC

A ranar Talata ne wata kotu ta bawa INEC umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan bayan jam'iyyar APC da gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, sun shigar da korafi.

Sai dai INEC ta shigar da korafi gaban wata kotun Abuja domin kalubalantar hukuncin kotun farko.

DUBA WANNAN: Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi zuwa N30,000

Jam'iyyar PDP ce a kan gaba da ma fi rinjayen kuri'un da aka kada a zaben farko na ranar 9 ga watan Maris da na ranar 23 ga wata.

Tuni dai jam'iyyar PDP da ragowar jama'a ke korafi a kan kin bayyana dan takarar jam'iyyar PDP, Bala Mohammed, a matsayin wanda ya lashe zaben da INEC ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel