Babbar magana: An dakatar da Osita Chidoka, mai magana da yawun Atiku Abubakar

Babbar magana: An dakatar da Osita Chidoka, mai magana da yawun Atiku Abubakar

- Sarkin garin Obosi da ke a jihar Anambra ya dakatar da Chief Osita Chidoka, kakakin Atiku Abubakar, daga cikin 'yan majalisar masarautar garin

- An dakatar da Chief Chidoka tare da wasu mutane ukku bisa zarginsu da kawo gawar wasu matasan garin Obosi guda biyu cikin fadar, da aka kashe su a zaben da ya gabata

- Sai dai Mgbakaogu, daya daga cikin wadanda aka dakatar, ya yi watsi da wannan labarin dakatarwar a matsayin shirme, yana mai cewa har yanzu shi ne (Atta Obosi)

Sarkin garin Obosi da ke a jihar Anambra, Igwe Chidubem Iweka II, ya dakatar da Chief Osita Chidoka, wanda kuma ya taba rike mukamin ministan sufurin jiragen sama kuma kakakin ofishin yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, daga cikin 'yan majalisar masarautar garin.

Iweka ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a karshen makon da ya gabata, inda ya bayyana korar Chidoka da wasu mutane biyu, Chief Linus Mgbakaogu da Chief Hyacinth Udemba, bisa zarginsu da kawo gawar wasu matasan garin Obosi guda biyu cikin fadar, da aka kashe su a ranar 9 ga watan Maris.

Sanarwar dauke da sa hannun Dr Benneth Mozie a madadin sarkin da sauran 'yan majalisar masarautar, ta ce wannan mataki da mutanen ukku suka yi na shigo da gawar cikin fadar ya sabawa al'adar masarautar Obosi wacce ta haramtawa sarki da 'yan majalisunsa ganin gawar mutane.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yadda gobara mai karfi ta babbake shaguna da wani gida a Kano

Babbar magana: An dakatar da Osita Chidoka, mai magana da yawun Atiku Abubakar
Babbar magana: An dakatar da Osita Chidoka, mai magana da yawun Atiku Abubakar
Asali: UGC

Sai dai, Chief Anthony Nwabude, babban firimiyan masarautar Obosi (Onowu Obosi), wanda ya halarci zaman fadar a lokacin da aka sanar da dakatarwar, ya shaidawa manema labarai cewa ba a samu wani lokaci na bitar sanarwarba ko kuma yin muhawarar hukuncin a tsakanin 'yan majalisar masarautar.

Nwabude, daya daga cikin tsofaffin mambobin majalisar masarautar, ya ce ba zai iya zaunawa ya kalli wannan hukuncin ba tare da ya ce uffan ba ganin cewa sam lamarin bai shafe shi ba.

A nashi bangare, Mgbakaogu, daya daga cikin wadanda aka dakatar, ya yi watsi da wannan labarin dakatarwar a matsayin shirme, yana mai cewa har yanzu shi ne (Atta Obosi) kuma zai ci gaba da kasancewa a mukamin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel