Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi zuwa N30,000

Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi zuwa N30,000

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kwamitin bayar da shawara a kan yadda za a fara biyan sabon karin albashi da majalisa ta amince da shi. Kwamitin ya mika rahoton ga shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

A ranar 9 watan Janairu ne shugaba Buhari ya kafa kwamitin karkashin jagorancin masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, bayan jaddada aniyar sa ta kara ma fi karancin albashin ma'aikata.

Shugaba Buhari ya fara bayyana niyyar sa ta yin karin albashi a watan Disamba na shekarar 2018 yayin gabatar da kasafin kudi a gaban mambobin majalisar tarayya.

Ya bayyana cewar kwamitin zai bawa gwamnati shawarwari a kan yadda zata samu sukunin biyan ma fi karancin albashin ba tare da an samu hauhawar farashin kayan masarufi da matsalar rage yawan ma'aikata ba.

Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi zuwa N30,000
Buhari yayin karbar rahoton kwamiti a kan karin albashi
Asali: Facebook

Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi zuwa N30,000
Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi
Asali: Facebook

Buhari ya karbi rahoton kwamiti a kan karin albashi zuwa N30,000
Buhari da mambobin kwamitin bayar da shawara a kan karin albashi
Asali: Facebook

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar mambobin majalisar wakilai da na majalisar dattijai sun yi bita tare da amincewa da biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi ga ma'aikata.

DUBA WANNAN: Buhari ya kafa kwamitin bitar aiyuka da tsare-tsaren gwamnatin sa

Sai dai ministan kasafi da tsare-tsare, Udo Udoma, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya zata kara yawan kudin haraji a kan kayan amfani domin samun kudaden da zata iya biyan sabon karin albashin.

Kalaman ministan sun jawo wa gwamnatin tarayya suka daga kungiyoyi daban-daban, musamman kungiyar kwadago ta kasa (NLC), wacce ta gargadi gwamnatin a kan batun karin harajin tare da yin kira gare ta da ta gaggauta fara biyan sabon albashin kafin watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel