Shugabancin Majalisa: APC zata fuskanci kalubale idan ta ki rabon mukamai a tsakanin yankuna - Jibrin

Shugabancin Majalisa: APC zata fuskanci kalubale idan ta ki rabon mukamai a tsakanin yankuna - Jibrin

Tsohon shugaban kwamitin majalisan wakilai kan kasafin kudi, Abdulmumin Jibrin, yayi gargadin cewa jam’iyyar APC zata fuskanci kalubale sosai idan ta gaza kasafta mukaman shugabancin majalisar dokokin kasar a tsakanin yankuna.

A baya jam’iyyar APC ta fuskanci kalubale wajen fidda tsari kan yanda zata raba mukaman majalisa ga yankuna, bayan tayi nasarar lashe kujeru mafi rinjaye a majalisa wanda yayi sanadiyyan haifar da rashin jituwa a dangantakar da ke tsakanin majalisan zartarwa da yan majalisar dokoki.

Yayinda yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen makon da ya gabata, Jibrin wanda ya kasance daraktan sadarwa a kungiyar kamfen din APC na matasa da mata, ya ce akwai bukatar aiwatar da hakana kamar yanda ake yi a sauran kasashen damokardiyya don zaban shuwagabannin majalisan kasa.

Shugabancin Majalisa: APC zata fuskanci kalubale idan ta ki rabon mukamai a tsakanin yankuna - Jibrin
Shugabancin Majalisa: APC zata fuskanci kalubale idan ta ki rabon mukamai a tsakanin yankuna - Jibrin
Asali: Depositphotos

Duk da haka yayi gargadin cewa kada sanatocin APC da mambobin majalisan wakilai su yarda jam’iyyar adawa (PDP) tayi amfani da su, kamar yanda ya faru a 2015 inda sanatan PDP ya riki mukamin mataimakin shugaban majalisar da yan APC suka rinjaya.

KU KARANTA KUMA: Al’umman Bauchi sun bukaci Gwamna Abubakar da ya rungumi kaddara akan kayen da ya sha a hannun PDP

Akan abunda ake zatto daga majalissar, yace: “Matsayar jam’iyya da shuwagabanninmu a koda yaushe shine cewa dukkan zababbun mambobin majalisar wakilai da sanatoci su kasance masu hakuri. Ana kan aiki, kuma ana nan ana tattaunawa."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel