Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da ke neman a dakatar da hada sakamakon Bauchi

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da ke neman a dakatar da hada sakamakon Bauchi

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, 25 ga watan Maris, ta yi watsi da karar da ke kalubalantar hukuncin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi.

Gwamna Mohammed Abubakar, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kalubalanci hukuncin INEC na tattara sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris a karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar.

Justis Inyang Ekwo, yayinda yake zartar da hukunci ya jingine umurnin farko da yayi na ranar 19 ga watan Maris, wacce ta dakatar da tartara sakamakon.

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da ke neman a dakatar da hada sakamakon Bauchi
Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da ke neman a dakatar da hada sakamakon Bauchi
Asali: Twitter

Alkalin ya yi umurnin cewa a bar INEC ta ci gaba da aikinta wanda kundin tsarin mulki ya bata dama.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Sanda sun kyale ‘Yan daba sun ci karensu babu babbaka a zaben Kano - CISLAC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, mutanen jihar Bauhi sun bukaci Gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar, wanda yayi takara akaro na biyu da ya rungumi kaddara.

Wannan shawara na zuwa ne jim kadan bayan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sakamakon zabe da aka sake a jihar, wanda ya nuna cewa Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben, inda suka bukace shi da yayi koyi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel