Al’umman Bauchi sun bukaci Gwamna Abubakar da ya rungumi kaddara akan kayen da ya sha a hannun PDP

Al’umman Bauchi sun bukaci Gwamna Abubakar da ya rungumi kaddara akan kayen da ya sha a hannun PDP

Mutanen jihar Bauhi sun bukaci Gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar, wanda yayi takara a karo na biyu da ya rungumi kaddara ya mika mulki ga dan takarar da yayi nasara a zaben da aka sake gudanarwa a jiha.

Wannan shawara na zuwa ne jim kadan bayan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sakamakon zabe da aka sake a jihar, wanda ya nuna cewa Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben, inda suka bukace shi da yayi koyi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2015.

Al’umman Bauchi sun bukaci Gwamna Abubakar da ya rungumi kaddara akan kayen da ya sha a hannun PDP
Al’umman Bauchi sun bukaci Gwamna Abubakar da ya rungumi kaddara akan kayen da ya sha a hannun PDP
Asali: Depositphotos

Mafi akasarin wadanda suka yi zaton Baturen zabe, Farfesa Kyari Mohammed zai sanar da wanda ya yayi nasara a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris tun a ranar Lahadi, basu ji dadi ba domin sai da suka jira umurnin kotu a ranar Litinin domin ta yanke hukunci kan yadda za a yi da sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa, kafin ta sanar da wanda ya yi nasa ko kuma za a sake zabe a yankin.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar PDP ya nufi kotu yayinda INEC ta kaddamar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zabe

Wadanda suka yi magana da majiyarmu a babban birnin jihar a ranar Lahadi sun nuna bacin ransu akan hukuncin jam’iyyar APC na cewa dan takaranta, Mohammed Abubakar ya tafi kotu, yayin da suka ce a bayyane ya san bai samu nasara ba, saboda haka ba zai tsira ba ko ya tafi kotu, saboda al’umma sun yanke shawara akan wanda suke son ya zama Gwamnan su.

Yayin da aka gama bayyana sakamakon, wassu magoya bayan jam’iyyar PDP sun nuna farin cikin su da wakoki a harabar Ofishin INEC, don yin murna akan sakamakon kanan hukumomi 19 cikin 20 da aka bayyana, cewa ranakun shugabanci APC a karkashin Mohammed Abubakar a jihar ta kare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel