Gobara ta lakume ajujuwan makaranta 7 a Kano

Gobara ta lakume ajujuwan makaranta 7 a Kano

- Gobara ta lashe ajujuwa bakwai a makaranta sakandare na Badawa da ke karanar hukumar Nassarawa a jihar Kano

- Lamarin ya afku ne da misalin karfe 1:30 na daren ranar Lahadi, 24 ga watan Maris

- Gobarar ta tashi ne sanadiyar wutar lantarki, kuma ba a rasa rai ba

Gobarar safiya ta lakume ajujuwan bakwai a makaranta sakandare na Badawa da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Kakakin rundunan yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a sakon waya a safiyar Litinin, 25 ga watan Maris ya ce ba a rasa rayuka ba a gobaran.

Gobara ta lakume ajujuwan karanta 7 a Kano
Gobara ta lakume ajujuwan karanta 7 a Kano
Asali: Twitter

Ya danganta lamarin ne ga wutar lantarki da ya taso daga dakin gwaje-gwaje na makarantar.

Ya ce gobaran ta fara ne misalin karfe 1:30 na tsakar dare.

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: PDP ta zamo mafi rinjaye a majalisar Bayelsa da kujeru 19 yayinda APC ke da 4

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Jihar Kano ta rincabe cikin dimuwa da zaman dar-dar yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta bayar da sanarwar gwamna Abdullahi Ganduje na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Biyo bayan zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa ta tabbatar da nasarar gwamnan Abdullahi Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar Kano a karo na biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel