Sake zabe: Jam’iyyar APC ta sake lashe wani kujeran majalisa a Osun

Sake zabe: Jam’iyyar APC ta sake lashe wani kujeran majalisa a Osun

- Jam' iyyar APC reshen jihar Osun ta sake lashe sauran kujeran da ya rage a majalisar dokokin jihar na mazabar Oriade a zaben da aka sake gudanarwa a ranar Asabar

- Sakamakon karshe da hukumar INEC ta saki ya nuna cewa APC na da kuri’u 12,088, yayinda PDP ta samu kuri’u 9,913

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun ta sake lashe sauran kujeran da ya rage a majalisar dokokin jihar kasar na mazabar Oriade a zaben da aka sake gudanarwa a ranar Asabar.

Da farko dai hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da zaben da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris a matsayin ba kammalalle ba.

Sake zabe: Jam’iyyar APC ta sake lashe wani kujeran majalisa a Osun
Sake zabe: Jam’iyyar APC ta sake lashe wani kujeran majalisa a Osun
Asali: Twitter

Hukumar zaben ta bayyana cewa ta kaddamar da zaben a matsayin ba kammalalle ba saboda tazarar da ke tsakanin wanda ya lashe zaben da babban abokin adawarsa bai kai yawan adadin kuri’un da aka soke ba.

A zaben da aka sake a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, dan takarar jam’iyyar APC, Babatunde Ojo ya samu kuri’u 702 inda ya doke babban abokin adawarsa na PDP, Pelumi Olajegbensi wanda samu kuri’u tara.

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: PDP ta zamo mafi rinjaye a majalisar Bayelsa da kujeru 19 yayinda APC ke da 4

Sakamakon karshe da hukumar INEC ta saki ya kama APC na da kuri’u 12,088, yayinda PDP ta samu kuri’u 9,913.

A baya APC ta lashe kujeru 22 cikin 26, inda jam’iyyar PDP ta tashi da kujeru uku kacal.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel