‘Yan Sanda sun kyale ‘Yan daba sun ci karensu babu babbaka a zaben Kano - CISLAC

‘Yan Sanda sun kyale ‘Yan daba sun ci karensu babu babbaka a zaben Kano - CISLAC

Wata kungiya mai zaman kan-ta mai suna Civil Society Legislative Advocacy Centre, CISLAC, ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda aka gudanar da zaben cike-gibi a jihar Kano cike da rikicin 'Yan daba.

Wannan kungiya tayi tir da yadda jami’an tsaro su ka gaza maganin rikicin daba da ya rincabe a lokacin zaben. Kungiyar tace masu kada kuri’a sun gamu da barazana iri-iri a wajen zaben da aka yi na cike gibi a Ranar Asabar 23 ga Watan Maris.

Kungiyar CISLAC ta kuma yi Allah-dai da kunnen kashi da hukumar INEC ta nuna a zaben inda ta cigaba da tattara kuri’u har ta sanar da sakamakon zaben jihar duk da cewa an koka da yadda aka gudanar da zaben a wurare da dama.

Shugaban wannan kungiya mai zaman kan-ta, ya bayyana cewa ya kamata ace hukumar zabe na kasa ta yi aiki da abin da sashe na 26 (1) na dokar ta ya nuna na cewa ayi wuf a dakatar da zabe idan har ta tabbata cewa rikici ya kaure a wuri.

KU KARANTA: Abin da na gani a zaben Gwamna da idanu na – Tsohon Sanatan Kano

‘Yan Sanda sun kyale ‘Yan daba sun ci kare su babbu babbaka a zaben Kano - CISLAC
CISLAC tace ‘Yan Sanda sun gaza maganin 'Yan daba zaben Kano
Asali: Depositphotos

Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani) yayi wannan jawabi ne a jiya Lahadi 24 ga Watan Maris da yamma. Mista Rafsanjani yace za a kafa mummunar dabi’a na amfani da daba wajen murde zabe idan har aka bar zaben na Kano ya zauna.

Shugaban wannan kungiya ya kuma soki yadda jami’an tsaro su ka nuna cewa babu wani rigima da aka samu a lokacin zaben, bayan kuma mursisi da INEC tayi wannan karo wajen tattara kuri’un Nasarawa akasin abin da ya faru a da.

A baya dai hukumar zabe ta soke zaben da aka yi a cikin Gama a dalilin rikici da ya barke. Wannan karo kuwa an sanar da zaben duk da cewa an samu lokacin da aka nemi Turawan zaben da takardun kuri’un aka rasa inji Auwal Rafsanjani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel