Harin Makiyaya ya salwantar da rayukan Mutane 2 a Nasarawa

Harin Makiyaya ya salwantar da rayukan Mutane 2 a Nasarawa

Mutane biyu sun riga mu gida gaskiya yayin da gidaje da dama gami da dukiya mai tarin yawa suka salwanta yayin aukuwar wani mummunan hari da ake zargin Makiyaya da zartas wa a karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Shafin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, ana zargin wani mummunan hari na Makiyaya ya salwantar da rayukan Mutane biyu gami da asarar muhallai da dukiya mai tarin yawa a karamar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Harin Makiyaya ya salwantar da rayukan Mutane 2 a Nasarawa
Harin Makiyaya ya salwantar da rayukan Mutane 2 a Nasarawa
Asali: Depositphotos

Daruruwan Mutane sun tsere daga muhallan su domin neman tsira yayin da Makiyaya suka zartar da ta'addanci kan wasu al'ummomi uku da ke karkashin karamar hukumar Akwanga a yankin Arewa ta Tsakiya.

Rahotanni sun bayyana cewa, hare-haren sun auku ba bu kakkautawa a tsakanin ranar Asabar da kuma Lahadi cikin kauyukan Mante da Nidam da ke yankin Akwanga a jihar ta Nasarawa.

Sarkin gargajiya na garin Akwanga mai masarautar Chun Mada, Samson Gamuyare, ya tabbatar da aukuwar wannan hari yayin ganawar sa da manema labarai inda ya ce a halin yanzu 'yan gudun hijira na kauyukan Mante da Nidam sun samu mafaka a garin Masarautar sa.

KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi: Masana'antar Kannywood ta taya gwamna Ganduje murnar samun nasara

Basaraken ya yi kira na neman daukin gaggawa daga hukumomi tsaro da masu ruwa da tsaki domin dawo da zaman lafiya da aminci na kwanciyar hankalin al'umma a yankin tare da saukaka ma su radadi na ibtila'in da ya auku.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel