Ba za mu bari jam'iyyar adawa ta kusanci jagoranci ba a Majalisar tarayya - Oshiomhole

Ba za mu bari jam'iyyar adawa ta kusanci jagoranci ba a Majalisar tarayya - Oshiomhole

A ranar Litinin 25 ga watan Maris, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya yi karin haske dangane da yadda jagoranci zai kasance a sabuwar majalisar tarayya ta 9 a tarihin Najeriya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Kwamared Oshiomhole ya ce jam'iyyar su ta APC ba za ta yi tarayya ba da jam'iyyar adawa ta PDP wajen jagoranci a sabuwar majalisar tarayya a wannan karo.

Kwamared Adams Oshiomhole
Kwamared Adams Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya ce jam'iyyar APC ba za ta lamunci abin da ya wakana a shekarar 2015 ya sake maimatuwa ba a wannan karo na 2019. Ya ce jam'iyyar a halin yanzu na bukatar hadin gwiwa a tsakanin mambobin ta wajen tabbatar da nagartaccen jagoranci mai aminci.

Kwamared Oshiomhole ya kara da cewa, jiga-jigan jam'iyyar APC za su aiwatar da bincike da tuntube-tuntube na diddigi tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin cimma matsaya ta yadda jagorancin majalisar tarayya zai kasance a sabuwar gwamnati.

KARANTA KUMA: Karashen zaben gwamnan jihar Kano cike ya ke da abin kunya - Obi

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kwamitin kamfe na Buhari ya shigar da karar jam'iyyar PDP a gaban hukumar 'yan sanda da zargin aikata laifi na leka bayanan sirri cikin na'urorin hukumar INEC ta barauniyar hanya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel