Karashen zaben gwamnan jihar Kano cike ya ke da abin kunya - Obi

Karashen zaben gwamnan jihar Kano cike ya ke da abin kunya - Obi

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Mista Peter Obi, ya bayyana takaicin sa kan zaben gwamnan jihar Kano da ya misalta shi a matsayin abin kunya.

Mista Obi ya ce zaben cike gurbi na gwamnan jihar Kano da ya gudana a ranar Asabar cike ya ke da ababe na mafi kololuwar abin kunya da ba za su taba kusantar wani mizani na gaskiya ko aminci ba.

Karashen zaben gwamnan jihar Kano cike ya ke da abin kunya - Obi
Karashen zaben gwamnan jihar Kano cike ya ke da abin kunya - Obi
Asali: Depositphotos

Obi cikin wata sanarwa da sanadin ofishin sa na sadarwa, a ranar Litinin ya ce ababen tur da Allah wadai da su wakana yayin zaben cike gurbi na gwamnan jihar Kano sun bayar da kofa bude tare da lasisi ga Matasa domin cin Karen su ba bu babbaka a fannin ta'addanci.

Ya ce a halin yanzu gwamnati ta bayar da wata kafa ta mummunar ta'ada irin ta dabanci da kuma murdiyar zabe ta kowane hali domin hawa kujerar mulki da a cewar sa hakan babbar barazana ce ga makomar kasar nan.

Tsohon gwamnan ya zargi hukumar jami'an tsaro ta 'yan sanda wajen taimakon 'yan daba da suka haddasa hauragiya ta muzantawa masu kada kuri'u a jihar Kano. Obi ya ce akwai bashi na bayanai domin wanke kanta da ya rataya a wuyan hukumar 'yan sandan jihar Kano.

KARANTA KUMA: Zan kara inganta kwararar romon dimokuradiyya a wa'adi na biyu - Ortom

Ya kuma bayyana takaicin sa dangane da rashin gaskiya gami da rashin adalci da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta gudanar yayin tattarawa da kuma bayyana sakamakon zaben ba bu tanadi na aminci.

Tsohon gwamna Obi ya jajanta tare da mika sakon sa na ta'aziyya ga 'yan uwa da abokanan arziki na wadanda rayukan su suka salwanta yayin zaben da ya gudana cikin jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel