Zan kara inganta kwararar romon dimokuradiyya a wa'adi na biyu - Ortom

Zan kara inganta kwararar romon dimokuradiyya a wa'adi na biyu - Ortom

- Gwamnan jihar Benuwai ya sha alwashin kara kaimi wajen inganta ci gaba da kuma kwararar romon dimokuradiyya jihar sa yayin wa'adin sa karo na biyu a kujerar gwamnati

- Samuel Ortom ya ce ba bu wanda za a bari a baya yayin karkatar da akalar sa ta jagoranci a karo na biyu

- Gwamna Ortom ya ce zai bai wa abokanan takarar sa dama ta bayar da gudunmuwa domin tabbatar da ci gaba a jihar.

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, bayan samun nasarar tazarce a kan kujerar sa, ya sha alwashin kara kaimi tare da hobbasa wajen tabbatar da ci gaba a jihar ta kowane fanni gami da inganta kwararar romon dimokuradiyya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamna Ortom ya yi wannan alkwari cikin fadar sa da ke birnin Makurdi yayin ganawa da manema labarai dangane da lashe zaben gwamna karo na biyu a ranar Lahadi, 24, ga watan Maris.

Gwamna Ortom tare da shugaban kasa Buhari
Gwamna Ortom tare da shugaban kasa Buhari
Asali: Twitter

Gwamna Ortom ya bayar da tabbacin cewar ba bu wanda zai bari a baya wajen tafiyar da sabuwar gwamnatin sa. Ya yi kira na neman hadin gwiwar wadanda su ka yi takara da shi domin ciyar da jihar Benuwai gaba.

Ba ya ga bayar da kofa bude ga dukkanin masu ruwa da tsaki, gwamna Ortom ya ce, wadanda suka yi takara da shi yayin zaben gwamnan jihar za su samu dama ta bayar da gudunmuwa komai kankanta domin fidda jihar Benuwai zuwa tudun tsira.

KARANTA KUMA: Saraki na fafutikar aiwatar da tasiri wajen samar da shugabanci a sabuwar Majalisar Dattawa

Yayin sadaukar da nasarar sa ga Mahallici da kuma al'ummar jihar Benuwai, gwamna Ortom ya kudiri aniyyar kara jajircewa wajen aiwatar da aiki tukuru tare da shan alwashi na gyara kura-kuran da gwamnatin sa ta yi a baya.

Ya yabawa kwazon hukumar zabe ya kasa mai zaman kanta watau INEC sakamakon ingataccen zabe da ta gudanar cikin zaman lafiya da aminci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel