Saraki na fafutikar aiwatar da tasiri wajen samar da shugabanci a sabuwar Majalisar Dattawa

Saraki na fafutikar aiwatar da tasiri wajen samar da shugabanci a sabuwar Majalisar Dattawa

A yayin da ake shirin rantsar da sabbin Sanatoci na sabuwar Majalisar Dattawa ta 9 a tarihin Najeriya, ana ci gaba da zargin shugaban majalisar dattawa na yanzu, Abubakar Bukola Saraki, da kulla wata kitimurmura yayin barin kujerar sa.

Shafin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, ana zargin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, da daura damarar yin tasiri wajen kafa jagoranci a sabuwar Majalisar dattawa yayin barin kujerar sa.

Shugaban Majalisar Dattawa; Abubakar Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa; Abubakar Bukola Saraki
Asali: Twitter

Zargin Saraki na yunkurin yin tasiri domin samar da jagoranci na shugaba da kuma mataimaki a sabuwar majalisar dattawa, ya haifar da dimuwa mai karfin gaske a zukatan manyan Sanatoci na jam'iyyar APC tare da hana su tsugunno.

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, cikin shirye-shiryen sa na tabbatar da wannan kudiri, Saraki a halin yanzu na jagorantar wata kungiya da ta hadar da jiga-jigan Sanatoci na jam'iyyar APC da kuma PDP domin cimma manufa kamar yadda ta kasance a 2015.

Ana ci gaba da zargin Saraki da kula kitimurmura ta amfani da shimfidar dabaru gami da tafarki da suka yi tasiri wajen kasancewar sa shugaban Majalisar dattawa, da kuma Ike Ekweremadu, a matsayin Mataimakin sa a 2015.

KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben jihar Kano ya gudana - INEC

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, Saraki domin tumke damarar sa ta cimma manufa, ya gudanar da wani taron a bayan Labule tare da zababbun Sanatoci 35 na jam'iyyar PDP a gidan sa da ke unguwar Maitama cikin birnin Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel