Zaben cike gurbi: Nasarar Ganduje ta haifar da dimuwa a jihar Kano

Zaben cike gurbi: Nasarar Ganduje ta haifar da dimuwa a jihar Kano

Jihar Kano ta rincabe cikin dimuwa da zaman dar-dar yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta bayar da sanarwar gwamna Abdullahi Ganduje na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Biyo bayan zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa ta tabbatar da nasarar gwamnan Abdullahi Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar Kano a karo na biyu.

Hukumar INEC a ranar Lahadi yayin bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ta ce, gwamna Ganduje ya sha kyar da gamayyar kuri'u 1,033,695 yayin da babban abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya tashi da kuri'u 1,024,713.

Zaben cike gurbi: Nasarar Ganduje ta haifar da dimuwa a jihar Kano
Zaben cike gurbi: Nasarar Ganduje ta haifar da dimuwa a jihar Kano
Asali: UGC

Baya ga kira na kaddamar da dan takarar ta a matsayin wanda ya lashe zabe, kuma duk da korafe-korafe akan magudin zabe, rikici gami da tarzoma da jam'iyyar PDP ta yi tare da neman a soke zabe, hukumar INEC ta yi burus na bayyana sakamakon zaben inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara.

Hakan ya faru a rana guda yayin da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, da kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, suka lashe zabukan cike gurbi da aka gudanar a jihohin su.

KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 7 a Diffa

A halin yanzu ana ci gaba da zaman dar-dar a jihar Kano, inda da dama daga cikin wuraren harkokin yau da kullum ka ma daga bude makarantu da kuma masana'antu suka gaza ci gaba da hada-hada kamar yadda suka saba domin fargaba ta abin da ka iya biyo baya.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, babbar jam'iyyar adawa ta PDP a ranar Lahadin da ta gabata, ta yi kira da cewar rashin tabbatar da nasarar dan takarar ta na gwamnan jihar Kano zai ci karo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel