Dan takarar PDP ya nufi kotu yayinda INEC ta kaddamar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zabe

Dan takarar PDP ya nufi kotu yayinda INEC ta kaddamar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zabe

- Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a jihar Plateau, Sanata Jeremiah Useni ya sha alwashin kalubalantar nasarar Gwamna Simon Lalong

- Lalong, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu kuri’u 595,582 inda Useni na PDP ya samu kuri’u 546,813

- Dan takarar na PDP ya yi godiya ga mutanen Plateau kan tarin goyon bayan da suka bashi da jam’iyyar a kokarinsu na nema wa kansu kyakyawar shugabanci

Sanata Jeremiah Useni, dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Plateau ya sha alwashin kalubalantar nasarar Gwamna Simon Lalong a karo na biyu.

A ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna bayan zaben da aka sake gudanarwa a ranar 23 ga watan Maris.

Dan takarar PDP ya nufi kotu yayinda INEC ta kaddamar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zabe
Dan takarar PDP ya nufi kotu yayinda INEC ta kaddamar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zabe
Asali: UGC

Lalong, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu kuri’u 595,582 inda Useni na PDP ya samu kuri’u 546,813.

Sai dai Useni ya bayyana cewa tawagarsa sun duba sakamakon da hukumar INEC ta saki da kuma takardun da jam’iyyar ta gabatar sannan kuma cewa akwai kokwanto.

Dan takarar na PDP ya yi godiya ga mutanen Plateau kan tarin goyon bayan da suka bashi da jam’iyyar a kokarinsu na nema wa kansu kyakyawar shugabanci.

KU KARANTA KUMA: PDP tace lallai Abba Yusuf ne ya lashe zaben gwamna a Kano

Useni ya bayyana cewa sun aikata haka, duk da tarin kalubale da suka fuskanta.

Ya kara da cewa jajircewarsu ya nuna abunda suke bukata karara na, don kawar da gwamnati mara tabuka komai sakamakon juyawa jin dadinsu da tsaro al’umma baya da tayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel