Sake zabe: PDP ta zamo mafi rinjaye a majalisar Bayelsa da kujeru 19 yayinda APC ke da 4

Sake zabe: PDP ta zamo mafi rinjaye a majalisar Bayelsa da kujeru 19 yayinda APC ke da 4

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zamo mafi rinjaye a majalisar dokokin jihar Bayelsa inda ta lashekujeru 19, yayinda jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tayi nasarar lashe kujeru hudu kacal daga cikin mazabu 24 da ke jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito craw hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) zuwa yanzu ta kammala zabe a mazabu 23 daga cikin 24 sannan an dakatar guda saboda umurnin kotu.

Mista Monday Udoh, kwamishinan zabe na Bayelsa, ya bayyana yayinda yake kaddamar da sakamakon zaben da aka sake a ranar Lahadi a Yenagoa, cewa PDP ta kayar da APC a mazabu biyu yayinda aka gudanar da zabe a ranar Asabar.

Sake zabe: PDP ta zamo mafi rinjaye a majalisar Bayelsa da kujeru 19 yayinda APC ke da 4
Sake zabe: PDP ta zamo mafi rinjaye a majalisar Bayelsa da kujeru 19 yayinda APC ke da 4
Asali: Facebook

“A yankin kudancin Ijaw IV, PDP ta samu kuri’u 27, 162 wajen yin nasara yayinda APC ta samu kuri’u 20, 886, sannan a mazabar Ogbia II, PDP ta samu 8, 984 inda ta kayar da APC wacceta samu 3, 038," inji kwamishinan zaben.

KU KARANTA KUMA: APC na kokarin shawo kan Gwamnoni domin samun shugabancin Majalisa

INEC ta bayyana cewa mazaba guda da ta rage shine Brass 1, kuma an dakatar biyo bayan umurnin da babbar kotun tarayya da ke Yenagoa ta bayar a ranar 22 ga watan Maris.

A cewar kwamishinan zaben, hukumar za ta sanar da masu ruwa da tsaki sannan ta saki sakamakon da zarar kotu tayi umurnin janye umurninta akan mazabar ta Brass 1.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel