A kamo mana Ambasada Ayo Oke da kuma Matar sa inji EFCC

A kamo mana Ambasada Ayo Oke da kuma Matar sa inji EFCC

Hukumar nan ta EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta bayyana cewa ta na neman tsohon shugaban hukumar NIA Ayodele Oke bisa zargin da ke kan su na satar dukiyar kasa.

EFCC ta bayyana wannan ne ta bakin mukaddashin Kakakin ta, Tony Orilade, a yau dinnan 25 ga Watan Maris kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust. Orilade yace tun kwanaki Kotu tace a damke sa.

EFCC tace har da Matar tsohon shugaban hukumar na NIA din watau Folasade Oke ake nema da zargin yin gaba da wasu kudi na $43,449,947, da £27,800 da kuma wasu N23,218,000 da EFCC su ka gano a Afrilun 2017.

KU KARANTA: Yadda za a kaucewa abin da ya auku a 2015 a Majalisa wannan karo

A kamo mana Ambasada Ayo Oke da kuma Matar sa inji EFCC
EFCC tana zargin Ambasada Ayo Oke da tafka mahaukaciyar sata
Asali: UGC

Bayan an samu wadannan makudan kudi na hukumar NIA a gidan Ayo Oke ne shugaban kasa Buhari ya tsige sa daga mukamin da yake kai. Daga baya kuma Alkali Chukwujeku Aneke ya bada umarni a cafke Ambasada Oke.

Tony Orilade yace tun a farkon Fabrairun 2019 wata Kotu a Legas ta bada umarni a damko Ayo Oke da Iyalin sa bayan sun halartar gayyatar da EFCC tayi masu domin su amsa wasu tambayoyi dangane da kudin da aka samu.

Akalla sau 2 kenan Ambasada Ayo Oke da Matar sa su na gujewa Kotu da kuma zaman da EFCC ta nemi tayi da su. A Nuwamban 2017, jami’an DSS ne su ka hana a shiga gidan tsohon babban shugaban hukumar tsaron kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel