An damke ma'aikatan asibiti 2 kan sayar da jariri

An damke ma'aikatan asibiti 2 kan sayar da jariri

Hukumar yan sandan jihar Legas ta damke wasu ma'aikatan asibitin Trinity Clinic dake Meiran, Legas kan zargin sayar da jaririn wata mata bayan sun yaudareta cewa jaririn bai zo da rai ba.

An tattaro cewa ma'aikatan asibitin, Mrs. Marbel Onochel da Dorcas Omitogun, sun sayarwa wata mata mai suna Mrs Helen Okoh jaririn a kudi N350,000.

Marbel da Dorcas sun bayyanawa iyayen jaririn cewa tuni sun birne jaririn saboda kawar musu da tunanin rasa dan jaririnsu.

Bayan wannan laifi na sayar da jarirai, an samu labarin cewa Onochel, wacce yar asalin jihar Delta ce tana da asibitin gargajiya a unguwar Meiran.

An damke ma'aikatan asibiti 2 kan sayar da jariri
An damke ma'aikatan asibiti 2 kan sayar da jariri
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ganduje ya ce zaben Kano Demokradiyya ce zalla, wadanda basu ji dadi ba suyi hakuri

Rikicin ya fara ne bayan iyalan mai jegon suka bayyana cewa lallai sai sun ga gawar jaririn da akace ya mutu, amma ma'aikatan asibitin suka gaza kawowa. Sai aka kai kara ofishin hukumar yan sanda.

Bayan gudanar da bincike kan Marbel da Dorcas, sun furta cewa lallai sun sayarwa Mrs Okoh jaririn. Yayinda Marbel ta dauki N250,000, ta baiwa Dorca, N100,000.

Yayin bincike, Mrs Okoh wacce ta siya jaririn ta bayyanawa hukuma cewa tana matuka bukatar haihuwa ne amma bata samu ba saboda tana fama da cutan "Fibroid".

Kakakin hukumar yan sanda, Bala Elkana, ya bayyanawa jaridar The Nation cewa an kwato jaririn daga hannun matar, an damke wacce ta siya jaririn da ma'aikatan asibitin kuma zasu gurfanar a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel