Abin da ya kai ni wajen Shugaban kasa Buhari – Inji Hon. Jibrin

Abin da ya kai ni wajen Shugaban kasa Buhari – Inji Hon. Jibrin

‘Dan Majalisar nan na yankin Kiru da Bebeji na jihar Kano watau Hon. Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa a cikin karshen makon jiya.

Honarabul Abdulmumin Jibrin ya bayyanawa manema labaran da ke cikin fadar shugaban kasar bayan ya fito cewa ya je wurin shugaba Muhammadu Buhari ne domin taya sa murnar lashe zaben shugaban kasa da yayi.

Sannan kuma ‘dan majalisar na jam’iyyar APC wanda aka dakatar kwanakin baya ya fadawa ‘yan jarida cewa ya ba shugaban kasar shawara game da wasu abubuwa da su ka shafi shugabancin majalisar tarayya ta 9.

KU KARANTA: Abin da na gani a zaben Gwamna da idanu na – Tsohon Sanatan Kano

Abin da ya kai ni wajen Shugaban kasa Buhari – Inji Hon. Jibrin
Jibrin yace dole a gujewa mai-man abin da ya faru a 2015 a Majalisa
Asali: UGC

Honarabul Jibrin yace ya nunawa shugaba Buhari yadda za a gujewa matsalar da jam’iyyar APC mai mulki ta shiga bayan an lashe zaben 2015 a dalilin zaben shugabannin da za su jagoranci ragamar majalisar tarayyar.

‘Dan majalisar ya kuma tabbatar da matsayar duk ‘yan majalisar APC na ganin cewa ba su hada-kai da wasu wajen yi wa ‘yan adawa aiki ba. A 2015, wasu Sanatocin APC sun hada kai da PDP wajen kawo majalisar dattawa.

Haka kuma babban ‘Dan majalisar na Kiru da Bebeji yake cewa akwai bukatar a kasa kujerun majalisar ta yadda za a samu raguwar masu neman takara bayan an yi masa tambaya a game da wannan batu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel