PDP tace lallai Abba Yusuf ne ya lashe zaben gwamna a Kano

PDP tace lallai Abba Yusuf ne ya lashe zaben gwamna a Kano

- Jam’iyyar PDP ta yi watsi da kaddamar da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a matsayin zababben gwamna da INEC tayi

- Jam’iyyar tace dan takararta, Abba K. Yusuf ne, asalin wanda ya lashe zaben da aka gudanar

- PDP ta bayyana zaben da aka sake a jihar a matsayin wani shiri na hada kai da aka yi tare da jami’an INEC wajen karkatar da kuri’u

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi watsi da kaddamar da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tayi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Jam’iyyar tace dan takararta, Abba K. Yusuf, ne sahihin wanda ya lashe zaben da aka yi, cewa duk wani kaddamarwa sabanin haka ba zai yi tasiri ba.

PDP tace lallai Abba Yusuf ne ya lashe zaben gwamna a Kano
PDP tace lallai Abba Yusuf ne ya lashe zaben gwamna a Kano
Asali: UGC

A wani jawabi da babban sakataren jam’iyyar na kasa, Kola Ologbodiyan ya aike zuwa ga manema labarai, a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris ya bayyana zaben da aka zake a jihar a matsayin karkatar da adadin kuri’u wanda jami’an INEC suka yi.

Hukumar INEC ta kaddamar da Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben da aka sake yi a jihar bayan tattara sakamako daga mazabun da aka gudanar da kananan hukumomi a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Benue ta doshi kotu

A cewar hukumar zaben, PDP ta samu kuriu’u 10,239 yayinda APC ta samu 45,876 a zaben da aka sake.

Baturen zaben jihar, Farfesa Bello Shehu, ya sanar da cewa gaba daya Ganduje ya samu kuri’u 1,033,695 yayinda babban abokin adawarsa, Abba Yusuf ya samu kuri’u 1,024,713.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel