APC na kokarin shawo kan Gwamnoni domin samun shugabancin Majalisa

APC na kokarin shawo kan Gwamnoni domin samun shugabancin Majalisa

Shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta fara shawo kan zababbun gwamnoni a karkashinta da kuma manyan jiga- jigan jam’iyyar domin tabbatar da shugabannin majalisar dokokin kasar sun kasance masu biyayya.

Majoyoyi sun bayyana cewa mambobin jam’iyyar APC a majalisun kasar biyu, harda sabbin shiga da shugabannin jam’iyyar a Abuja, na kokarin neman mafita gabannin rantsar da zababbun yan majalisar dokokin kasar.

An tattaro cewa an shawarci zababbun gwamnoni a karkashin jam’iyyar APC da su yi aiki tare da sanatoci da yan majalisar wakilai daga jihohinsu domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a majalisar dokokin kasar.

APC na kokarin shawo kan Gwamnoni domin samun shugabancin Majalisa
APC na kokarin shawo kan Gwamnoni domin samun shugabancin Majalisa
Asali: Twitter

An tattaro cewa yunkurin ya biyo bayan wani makirci da Shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Bukola Saraki ke yi, na son yin kutun-kutun wajen zabar sabon Shugaban majalisar a lokacin da za a rantsar da majalisar dattawa ta tara a watan Yunin wannan shekarar.

Rahoto ya nuna cewa kungiyar Saraki sun gana a makon da ya gabata a gidansa da ke Maitama inda zababbun sanatocin PDP 35 suka amince da hada kai wajen billowar sabun Shugaban majalisar dattawa da kuma maye matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Benue ta doshi kotu

Ku giyar, wacce aka ce sa samo mafita uku, za ta aiwatar da daya daga cikinsu kan matsayin Shugaban majalisar dattawa idan mabobin APC biyu ko fiye da ahakan suka gabatar da kansu ga matsayin a zauren majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel