Zaben 2019: Ganduje, Tambuwal, Lalong, Ortom sun yi tazarce

Zaben 2019: Ganduje, Tambuwal, Lalong, Ortom sun yi tazarce

Gwamnonin jihar Kano, Sokoto, Plateau da Benue a ranar Asabar sun samu nasarar lashe zaben kujeran gwamna karo na biyu. Amma gwamnonin jihar Bauchi da Adamawa na cikin tsaka mai wuya yayinda ake sauraron hukuncin kotu.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da takwararsa na jihar Plateau, Simon Bako Lalong sunn samu nasarar zarcewa karkashin tutar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakazalika gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto da takwararsa na Benue, Samuel Ortom suka samu zarcewa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA: An fara sakin sakamakon zaben cike-gurbi na Gwamna

Zaben 2019: Ganduje, Tambuwal, Lalong, Ortom sun yi tazarce
Zaben 2019: Ganduje, Tambuwal, Lalong, Ortom sun yi tazarce
Asali: Facebook

Dukkansu sunyi musharara a zaben gwamnan 9 ga watan Maris da aka gudanar a jihohi 29 amma sakamakon zaben jihar Kano, Sokoto, Benue, Bauchi da Adamawa ya nuna cewa ba za a samu zakara a lokacin ba sai an sake lale. Jihar Rivers kuwa, an dakatar saboda rikice-rikice.

Duk da zagayen zabe na biyu da akayi ranar Asabar, 23 ga watam ba a samu zakara ba a jihar Bauchi saboda gwamna Mohammed Abubakar na jam'iyyar APC ya shigar da kara kotu kan sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa wanda yanuna abokin hamayyarsa, Bala Mohammed na nasara.

Hakazalika a jihar Adamawa, kotu ta dakatad da zaben jihar saboda karar da wanin dan takara ya shigar cewa ba'a sanya jam'iyyarsa a cikin takardar kuri'a ba, saboda haka akwai yiwuwan sake zaben daga farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel